1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yar Chibok ta mika kanta ga sojoji

Abdul-raheem Hassan
August 8, 2021

Daya daga cikin 'yan matan makarantar Chibok da mayakan Boko Haram suka sace sama da shekaru bakwai a jihar Borno, ta koma cikin iyayenta bayan mika kanta da mijinta ga jami'an tsaron Najeriya.

https://p.dw.com/p/3yhbE
Screenshot mutmaßliches Boko Haram Video
Hoto: youtube/Fgghhfc Ffhjjj

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya ce a Yuli ne tsohuwar dalibar mai suna Ruth Ngladar Pogu, ta yi saranda ga sojojin Najeriya tare da daya daga cikin dan Boko Haram da ya aureta.

Akalla dalibai 300 'yan shekaru 12 zuwa 17 ne mayakan Boko Haram suka kwashe a watan Afirilu a shekarar 2014 a makarantar sakadaren Chibok da ke jihar Borno Arewa maso gabashin Najeriya, matakin da ya haddasa zazzafar martani a ciki da wajen kasar tare da matsawa gwamnatin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na kubutar da daliban.

Sai dai har yanzu akwai alamar tambaya kan batun tsaro musamman ga makarantun boko, ganin yadda masu garkuwa don neman kudin fansa ke rike da daruruwan dalibai arewacin kasar.