Yar Adua ya lashe zaben shugaban kasa a Nigeria | Labarai | DW | 24.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yar Adua ya lashe zaben shugaban kasa a Nigeria

Zababben shugaban kasa a tarayyar Nigeria yayi kira ga alummomin kasar dasu hada kai domin dorewar cigaba,adai dai lokacin da yan adawa ke barazanar shigar da kara gaban kotu domin kalaubalantarsa,a zaben shugaban kasar daya samu suka daga cikin kasar da ketare.Umaru Musa Yar adua a hirar ta farko da manema Labaru a birnin Abuja a daren jiya,yayi ki ga alummar Nigeria dasuyi laakari dacewa anyi gwargwamaya kuma an kare,ya kamat dukkan wasu banbance bance dake tsakaninsu ,su kasance tarihi.Yar Aduan dake zama gwamnan Jihar Katsina dai bya samu nasarar tsayawa neman kujerar shugaban Nigeria bisa ga goyon bayan shugaba Obasanjo mai barin gado.

Hukumar zabe mai zaman kianta ta INec ta sanar dacewa Yar Aduwa ya samu nasara bisa ga manyan abokan adawarsa biyu ne da yawan kuriu million 24 da dubu dari 6.