′Yansanda sun killace dandalin shaƙatawa na Times square dake New York ta Amirka | Labarai | DW | 02.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yansanda sun killace dandalin shaƙatawa na Times square dake New York ta Amirka

Shugaban Amirka Barack Obama ya yaba da matakin karta kwana da 'yansanda suka ɗauka na killace yankin domin ceto rayukan Jama'a.

default

Shugaban Amirka Barack Obama

Hukumomin 'yansanda a birnin New York ta Amirka suna binciken wata mota da akace tana shaƙe da Bama-bamai a wata cibiyar shaƙatawa ta Times Square dake tsakiyar birnin.

Tuni dai jamai'an tsaron suka killace ɗokacin yankin da aka ajiye motar tare kuma da gudanar da bincike. Kanfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa anga wani mutun yana gudu daga inda motar ke ajiya.

Jami'an kwanana dai sunce sungano na'urorin Bama-bamai tare da manfetur da wasu sinadarai na haɗa nakiyoyi a motar.

Shugaban Amirka Barack Obama wanda aka sanar dashi aukuwan wannan lamari ya yaba da matakin karta kwana da 'yansanda suka ɗauka na killace yankin domin ceto rayukan Jama'a.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Abdullahi Tanko Bala