Yankin Kataloniya zai tsahirta ficewa | Labarai | DW | 11.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yankin Kataloniya zai tsahirta ficewa

A cewar Puigdemont kuri'ar raba gardamar da aka kada daya ga watan nan na Oktoba ta bawa yankin halascin fita daga Spain sai dai za su tsahirta.

Spanien Parlament in Barcelona Carles Puigdemont (Getty Images/D. Ramos)

Shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemont

Shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemont, a ranar Talata ya bayyana dakatar da shirin ballewar yankin daga Spain sai dai ya bayyana bukata ta zaman tattaunawa a matsayin mataki da zai sanya yankin kama hanyar ficewa daga kasar Spain.

A cewar Puigdemont kuri'ar raba gardamar da aka kada daya ga watan nan na Oktoba ta bawa yankin dama na cin gashin kai sai dai za a dakatar da yin hakan har sai an sake tattaunawa da mahukuntan Madrid.

Yanzu dai hankali ya karkata kan gwamnatin tsakiya inda a wannan rana ta Laraba Firmanista Mariano Rajoy ya kira taron majalisar ministocinsa cikin gaggawa, bayan da a baya ya yi watsi da duk wata tattaunawa da masu rajin ballewar.