1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kungiya mai kwatarwa mata da marayu hakkinsu

February 23, 2021

Kungiyar Widow and Orphans Movement na aikin fafutukar kare hakkin marayu da mata da mazajensu suka mutu a Ghana. Yanzu ta samu nasarar sauya tsohuwar al'adar nan ta hana mata da yara kanana gado.

https://p.dw.com/p/3pkku
Überschwemmung in Nordindien Uttarakhand
Mata da mazajensu suka mutu a IndiyaHoto: DW/Murali Krishnan

A yankin Upper East a kasar Ghana mata ba su da ikon gadon abin da mazajensu suka bar masu, sai dai tun a shekara ta 1985 gwamnati ta kirkiro wata doka da ta bai wa mata damar yin gado amma al'ummar yankin ba sa amfani da wannan ayar dokar. Kimanin mata sama da dari bakwai aka yi nasarar kwato wa gadonsu, sai dai akwai sauran jan aiki a gaba inda mata sama da dubu hamsin ke kukan an danne musu hakkokinsu a yankin.

Amma yanzu wasu jajirtattun mata a yankin sun kafa wata sabuwar kungiya, mai suna Widow and Orphans Movement wadda ta tsaya kai da fata sai an fara amfani da wannan doka da aka yi watsi da ita kimanin shekaru talatin da biyar da samar da ita. Tani na cikin wadanda kungiya ta kwato wa hakkinta da ke cewa ''Sai ka wahala kai da mijinka wajen gina gida ko mallakar fili, amma da mai gidan naka ya mutu sai yan uwansa su karbe komai. amma yanzu da zuwan wannan kungiyar komi ya sauya.''

Christiana da ke zama makwabciyar Tani wadda kuma ta yi sabon aure ta ce wannan al'ada na tada mata hankali tana mai cewa.''Sam tsarin bai yi ba, duk irin wahalar da ka sha tare da mijinka, sai bayan ya mutu kaninsa ya tuma gefe guda ya ce bai kamata ka gaji wannan ba ko wancan.''

Akwai alamu na samun sauyin wannan mummunar al'adar da aka gada kaka da kakanni bayan kafuwar wannan kungiyar da ke wayarwa mata a yankin kai kan yin watsi da hana mata gado. Fati Abigail Abdullahi wata yar fafutuka a yankin na Upper East da ke Ghana na kan gaba wajen yin wannan kiran. Ta ce ''Akwai shi a cikin dokokin kasar Ghana wanda ya bayyana karara yadda za a yi gado.''Sai har yanzu akwai wasu masu tunanin mutanen jiya da ke adawa da bai wa matan gado, Tei Gorog na daya daga cikinsu, ya ce '' Idan mace ta gaji gida ko filin mijinta to tana iya sayar da shi ta je ta auri wani mijin kuma ta watsar da yaran da aka bar mata.''