Yankin arewa maso gabashin Najeriya na taron haɓaka tattalin arziƙi | Siyasa | DW | 03.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yankin arewa maso gabashin Najeriya na taron haɓaka tattalin arziƙi

Taron wanda ya sami halartar shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da sauran manyan baƙi ya mayar da hankali kan harkokin inganta noma da illimi da ayyukan yi waɗanda za su magance matsalolin yankin

A wani abun dake zaman kama hanyar fiskantar sabbabbi na dabaru a ƙoƙarin shawo kan matsalolin tsaro da sukai aure suka tare a yankin Arewa maso gabashin tarrayar Najeriya, masu ruwa da tsaki da makomar yankin na can na taro a garin Gombe domin nazarin sabbabin dabarun amfani da albarkatun da Allah ya huwace, domin rage raɗaɗin na tashe-tashen hankula.

Sannu a hankali dai ɗan hakin da ka raina na neman tsone ido, sannu a hankali kuma ido na buɗewa game da rashin alfanun ƙarfi na hatsi ga ƙoƙarin yaƙar annobar boko haram da ta tada hankula kuma ke barazana ga makomar ɗaukacin tarrayar Najeriya.

Ko da sanyin safiyar jiya Litinin, (02-12-2013) dai an wayi gari da harin dake zaman irin sa na farko da ya kai har ga ƙona jiragen yaƙi sannan kuma ya tabbatar da irin tasiri na ƙungiyar da ta sha lugude na sojan ƙasar ta Najeriya, amma kuma ke nuna alamar komawa da shi mai rai har guda tara.

To sai dai kuma can a yankin na Arewa maso gabas dake na kan gaba ga matsalar rashin tsaron dai, ƙwai da kwarkwatar yan yankin na can na kallon sabbabi na dabaru da nufin amfani da damammaki na noma da ilimi dama aiyyukan yi da nufin yaƙar annobar da ake ta'allaƙawa da zaman ummul'abasin matsalar ta rashin tsaro.

Kabir Ahmed dai na zaman shugaban haɗa taron da ya samu halartar manya na 'yan siyasa da ma 'yan bokon da yanzu haka ke tunanin haɗa gwiwa da nufin tnkarar manufa ɗaya tilo a tsakanin al'ummar yankin. Kuma a faɗarsa samar da sana'a na zaman mafita ga barazanar da yankin ke fuskanta.

Manufar taron tattalin arziƙin

DW_Nigeria_Integration2

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Taron dake zaman irin sa na biyu da kuma ke zuwa a dai dai lokacin da halin na tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a cikin yankin da,i na nuna irin jan aikin dake gaban yankin da ko bayan batun na rashin tsaro ke zaman na baya ga dangi ga batun matsalar rashin ilimi da mutuwa ta yara kanana dama fatara da talaucin al'ummarta.

To sai dai kuma yankin na zaman ɗaya daga cikin na kan gaba ga batun albarkatu na noman dake iya maida shi na kan gaba ga batun rayuwa dama cigaban al'umma, in banda jerin ƙalubale na rashin kuɗi da ma gazawar gwamnatoci na bada kariya ga manoman yankin a faɗar Sulaiman Baba dake zaman mataimakin zaunnanen sakataren ma'aikatar gona ta jihar Adamawa.

To sai dai kuma wane irin tasiri sabon yunƙurin ke iya yi ga ƙoƙarin ganin bayan matsalar ta tsaro dai a faɗar Mohammed Magaji Gombe dake zaman wani mai sana'ar noma mafita na zaman taimakawa manoma da masu sana'ar kiwo a cikin yankin.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin na cikin sabbabin dabarun da shugabannin yankin na tunanin ke zaman mafita a cikin rikici.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Pinaɗo Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin