Yanke hukunci ga matuƙin jirgin ruwa | Labarai | DW | 11.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yanke hukunci ga matuƙin jirgin ruwa

Wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke wa matuƙin jirgin ruwan nan da ya yi haɗari a watan Afrilun da ya gabata Lee Jun-Seok hukuncin ɗaurin shekaru 36 a gidan kaso.

Haɗarin da ya afku a ranar 16 ga watan na Afrilu ya yi sanadiyyar asara rayukan mutane 300 mafi yawansu yara dalibai 'yan makaranta. An dai gano gawarwaki 295 yayin da har yanzu ake neman sauran mutane 10 da suma ake tsammanin sun hallaka a tekun. Kotun dai ta samu matuƙin jirgin ruwan Lee Jun-Seok da laifin ganganci yayin da ta wanke shi daga zargin kisan kai da gan-gan. Masu bincike dai sun bayyana cewar ga dukkan alamu an ɗauki fasinjojin da suka wuce kima a cikin jirgin, wanda a cewar su hakan ya taimaka wajen afkuwar haɗarin.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane