Yanayin Muhallin Afirka--Barazana ga Dausayi | Learning by Ear | DW | 29.01.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Yanayin Muhallin Afirka--Barazana ga Dausayi

default

Yanayin Muhallin Afirka--Barazana ga Dausayi

Ƙasashen Afirka ne suka fi ba da ƙarancin gudummuwa wajen gurɓata muhalli ta hanyar hayaƙin da ke bazuwa a sararin samaniya daga manyan masana’antu, amma an lura cewa illar da take haifarwa, tafi shafar ƙasashen Afirka musamman in an yi la’akari da yadda ake rasa duk wani yanayi na rayuwa. Shirin Ji Ka Ƙaru zai duba dangantakar al’umma da yanayin muhalli a Afirka.

A nan za mu lura da cewa ɗan Adam na sare itatuwa domin ya yi noma, mutane na kamun kifi da farauta a duk inda suka samu damar yin haka a ko’ina.

An lura cewa dagwalon masana’antu duk ya mamaye garuruwan da jama’a suke, ga tsadar rayuwa in har za a kauda irin wannan barazana. Abin takaicin yanzu kowa na so ya mallaki mota ta shiga wanda hakan ke ƙara kawo gurɓatar yanayi saboda hayaƙin da motocin ke fitarwa.

Gurɓatar Yanayi

Gurɓacewar yanayi yanzu ya zama ruwan dare, a duk faɗin duniya.

Ana samun ƙarancin ruwan sama a ko’ina, yanayin zafi sai ƙaruwa yake a yayin da ake ƙarancin ruwan sha da ake amfani da shi na yau da kullum. Jama’ar da abin ya fi shafa su ne na karkara, ba su iya noma abin da za su ci ba su da kuma isasshen ruwa na sha a rayu, daɗin daɗawa yanzu dausayin da aka saba ana amfanarsa da dazuzzuka da ake kiwo yanzu suna barazanar ɓacewa baki ɗaya.

Shimfiɗa sabbin matakai

Ban da kawo muku abubuwan da ke ƙalubalantar gurɓacewar yanayin muhalli, Shirin Ji Ka Ƙaru zai fito da sabbin dabaru na zamani. Za’a nuna wasan kwaikwayo inda wasu yara matasa huɗu ‘yan makaranta suka shiga duniya domin su san irin halin yanayin da suka samu kansu a ciki. Za a bi su muga yadda rayuwar tasu za ta kasance.

An yi shirin na Ji ka ƙaru a harsuna shidda, waɗanda suka haɗa da Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portuguese, da Amharic.

Shirin Ji ka Ƙaru na samun gudunmuwa ne daga Ofishin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Jamus.

Sauti da bidiyo akan labarin