′Yan Turkiya sun isa gida daga Iraƙi | Labarai | DW | 20.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Turkiya sun isa gida daga Iraƙi

Bayan kwashe watanni a hannun yan ta'adda waɗanda suka mamaye arewacin Iraƙi, yanzu iyalai sai murna suke yi da sakin 'yan uwansu.

Turkawa 49 da Ƙungiyar IS ta kama a arewacin Iraƙi watanni uku da suka gabata, sun samu kuɓuta kuma sun isa gida lafiya kamar yadda Firaministan ƙasar ya ba da sanarwa.daga cikin mutanen da aka sace har'da wasu jami'an diflomasiyya da sojoji da yara ƙanana. A watan Juni ne dai aka sace mutanen cikin ƙaramin ofishin jakadancin Turkiya da ke Mosul. Gudun taɓa lafiyar mutanen ya hana Turkiya haɗa gwiwa a shirin Amirka na yaƙi da 'yan ta'addar wanda duniya ke shirin yi musu taron dangi.