1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana gudanar da zanga-zanga a Tunisiya

September 26, 2021

Daruruwan masu zanga-zanga a birnin Tunis na Tunisiya sun bazama kan titi inda suke nuna fushinsu kan kwace ikon gwamnati da Shugaban Kasar Kais Saied ya yi. Sun bukaci shugaban da ya yi gaggawar sauka daga mulki.

https://p.dw.com/p/40sf3
Tunisien Protest gegen Präsident  Kais Saied
Hoto: Yassine Gaidi/AA/picture alliance

A cikin makon nan mai karewa ne dai Kais Saied ya jingine tsarin mulkin Tunisiya na shekara ta 2014, inda daga yanzu ya kuduri aniyar amfani da dokar ''decree'' tamkar ta soja wurin tafiyar da gwamnati. A watan Yulin da ya gabata kuma ya sauke firaministan kasar daga mulki, sannan ya dakatar da aikin majalisar kasar.

Sai dai masu zanga-zangar ta wannan Lahadai sun taru a titin Habib Bourguiba Avenue na birnin Tunis, inda a nan ne zanga-zangar da ta kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Marigayi Zine El Abidine Ben Ali ta samo asali, suna masu cewa yanzu shi ma shugaba mai ci a Tunisiyan sun ya tafarkin shugabanni masu mulkin kama-karya.