1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Syriya sun bukaci makamai

April 10, 2013

Masu fafutukar neman sauyi na Syriya sun mikawa sakataren wajen Amurka John Kerry bukatarsu ta samun tallafin makaman da za su basu damar hambarar da Bashar al-Assad.

https://p.dw.com/p/18DuI
Hoto: AFP/Getty Images

'Yan tawayen Siriya sun mika kokon bararsu ga sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na a tallafa mu su da makamai domin cigaba da fafautukar da su ke ta kokarin kawar da shugaba Bashar al-Assad daga gadon mulki. Sun mika wannan bukata ce yayin wani taro da su ka yi da ministocin harkokin wajen kasashen nan takwas masu karfin masana'antu na G8 da kuma sakataren harkokin wajen Amurka a wannan Larabar a birnin London na Burtaniya.

Sai dai hakar ba ta kai ga cimma ruwa domin sakataren na harkokin wajen Amurka bai amince da wannan bukata kana mahalarta taron sun nuna damuwarsu ta fadawar makaman hannun masu kaifin kishin addini da ke yankin musamman ma 'yan kungiyar Al-Qaida. Nan gaba kadan ne dai ake sa ran yin makamacin wannan taron inda 'yan kungiyar ta kawayen Siriya za su hallarta duka dai da mufin kashe wutar rikicin Siriyan.

Baya ga wannan, har wa yau an tabo batun shirin nukiliyar Iran wanda Amurka ta nuna damuwarta musamman ma dai saboda sabuwar tashar sarrafa Uraniyum din da Iran din ta gina.

Mawallafi: Ahmed Salisu

Edita: Mouhamadou Awal