′Yan tawayen Siriya na cin zarafin Kiristoci | Labarai | DW | 11.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawayen Siriya na cin zarafin Kiristoci

Kiristoci da ke ƙauyen Ma'alula wanda ya faɗa hannun masu kaifin kishin Islama, sun bada rahotonnin rayuwarsu na fiskantar hatsari

ARCHIV - Ein Kämpfer der Freien Syrischen Armee hält seine Maschinenpistole und ein abgefeuertes Artilleriegeschoss der Regierungstruppen in den Händen während er am 20.10.2012 durch die Straßen von Aleppo zieht. Obama erklärt die «Rote Linie» für überschritten: Wenige Tage vor dem G8-Gipfel sieht die US-Regierung den Einsatz von Giftgas durch das Regime in Syrien bestätigt. Jetzt will Washington die Rebellen militärisch unterstützen - auch mit Waffen, heißt es. EPA/CESARE QUINTO (zu dpa USA wollen Syriens Rebellen militärisch unterstützen vom 14.06.2013) +++(c) dpa - Bildfunk+++

Wani ɗan tawayen Siriya

'Yan tawayen ƙasar Siriya na ci gaba da kasancewa a cikin ƙauyen Ma'alula, wanda suka ƙwace tun ranar Lahdin da ta gabata. Ƙwanyen na Ma'alula wanda ke da tsohon tarihi, an bayyana cewa akwai mazaunansa Kiristoci kimanin dubu biyar. Kiristoci a ƙauyen sun bayyana cewa 'yan tawayen da ke gumshe da masu kaifin kishin Islama, waɗanda ke alaƙa da ƙungiyar Alƙa'ida, sun bayyana cewa ana tilastawa Kiristocin shiga addinin Musulci bisa ƙarfin tuwo. Tun da farko dai an bayyana cewa 'yan tawayen sun fice daga garin, amma rahotanni suka ce kawo yanzu akwai 'yan tawaye a birnin inda su ke lalata kayakin tarihi, kana suna cin zarafin duk wanda bai karɓi musulunci ba. 'Yan uwa da dangin Kiristoci da ke a gefen birnin, suna cike da ɗimuwa kan abinda kan iya samun 'yan uwansu Kiristoci da ke ƙauyen mai daɗaɗɗen tarihi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu