1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Seleka sun ƙwace babban birnin Bangui.

March 24, 2013

An hamɓarra da François Bozize daga karagar mulkin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/183Nq
Central African Republic President Francois Bozize arrives before the round table of the partners of the Central African Republic held in Brussels on June 17, 2011. AFP PHOTO JOHN THYS (Photo credit should read JOHN THYS/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images

Rahotani daga Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na cewar ƙungiyar yan' tawayen Seleka ta kutsa kai a cikin fadar shugaban ƙasa François Bozize wacce suka karɓi iko da ita, bayan gumurzun da suka sha da dakarun gwamnatin tun daren jiya.

A yayin da ya ke hira da DW, kakakin kungiyar tawayen Seleka Eric Massi ya tabbatar da nasarar juyin mulkin.

Yace: Dakarunmu sun kwace fadar shugaban kasa, da kuma mahimman ofisoshin gwamnati dake birnin Bangui.

Mun samu larabin cewar shugaba Bozize ya ranta cikin na kare. A yanzu mun shiga yunkurin tabbatar da tsaro cikin babban birnin Bangui.Ina amfani da wannan dama, domin miƙa kira ga duk al'umma gaba ɗaya, ta kwantar da hankali.

François Bozize wanda ya karɓi mulki da ƙarfin bindiga a shekara 2003,'yan tawayen na zarginsa da rashin mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar da suka rattaɓa wa hannu, a cikin wata Janairu da ya gabata a birnin Libreville na kasar Gabon.

Mawallafi: Abdourahmane Hassane.
Edita: Yahouza Sadissou Madobi