1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Mali sun kwace wasu yankunan da ke karkashin gwamnati

January 10, 2013

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci 'yan tawayen Mali su martaba yarjejeniyar tsagaita bude wutar da suka amince da ita a ranar 4 ga watan Disamba.

https://p.dw.com/p/17Hh8
Militiaman from the Ansar Dine Islamic group sit on a vehicle in Gao in northeastern Mali in this June 18, 2012 file photo. To match Special Report MALI-CRISIS/CRIME REUTERS/Adama Diarra/Files (MALI - Tags: CIVIL UNREST CRIME LAW POLITICS RELIGION)
Hoto: REUTERS

Kungiyar Ansar Dine da ke fafutukar wanzar da yin aiki da shari'ar Musulunci, kana ke da iko da yankin arewacin Mali, ta fadi cewar ta yi nasarar kwace iko da wasu yankunan da ke karkashin ikon gwamnati a tsakiyar kasar - a wannan Alhamis, tare da alwashin ci gaba da nausawa zuwa kudancin kasar. A cikin zantawar da Abdou Dardar, mai magana da yawun kungiyar yayi ta wayar tarho da kanfanin dillancin labaran Faransa daga birnin Bamako, fadar gwamnatin Mali, ya ce a yanzu dai mayakan kungiyar Ansar Dine na cikin birnin Konna, kuma su ne ke da iko da kusan daukacin birnin, wanda a da ke karkashin ikon dakarun gwamnati.

Tun dai a daren Larabar nan ce dakarun gwamnatin Mali ke ci gaba da fafatawa da 'yan tawayen da ke kula da harkokin mulki a yankin arewacin kasar.

A halin da ake ciki kuma Majalisar Dinki Duniya ta nuna damuwarta game da bata-kashin da ke ci gaba da wanzuwa a tsakanin dakarun gwamnatin Mali da kuma 'yan tawayen kasar, amma ta ce tana kokarin samo bakin zaren shawo kan matsalar ta hanyar siyasa. A cewar Martin Nesirky, kakakin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, a bisa wannan dalilin ne majalisar ke yin kira ga 'yan tawayen kasar ta Mali da su mutunta yarjejeniyar dakatar da kaddamar da farmakin da suka amince da ita a ranar hudu ga watan Disamba, da kuma wani kudirin kwamitin sulhun majalisar daya nemi su gujewa duk wani aikin ta'addanci a yankin. Nesirky ya ce Majalisar Dinkin Duniya dai na bayar da cikakken goyon bayanta ga shirin samar da zaman lafiyar da kungiyar tattalin arziki ta yankin yammacin Afirka ECOWAS ta tsara, kana tana fatan taron sulhun da aka tsara gudanarwa a ranar 21 ga wata Janairun nan, zai haifar da sakamako mai kyau.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal