′Yan tawayen gabacin Kongo na cikin duhu | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 25.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

'Yan tawayen gabacin Kongo na cikin duhu

Tun bayan fara tattauna batun sulhu da gwamnatin Kabila bayan ficewarsu daga garin Goma, 'yan tawayen kungiyar M23 ba su san alkiblar da aka nufa ba.

Bari mu fara da jaridar Die Tageszeitung wadda a labarinta mai taken "'Yan tawaye sun tashi a tutar babu" sai ta ci gaba kamar haka:

"'Yan tawayen kungiyar M23 a gabacin Kongo sun shiga mawuyacin hali a kokarin kafa hukumomin fararen hula a yankunansu. Ko da yake sun dakatar da yakin a yanzu, amma tambaya ita ce har zuwa yaushe? Yakin da 'yan tawayen dake karkashin jagorancin janar janar na kabilar Tutsi, suka fara a cikin watan Afrilun bara a kan gwamnatin Kongo ya kai su ga shiga garin Goma a cikin watan Nuwamba. Amma saboda matsin lamba daga kasashen duniya, sun fice daga garin kwanaki 10 bayan sun kwace shi daga hannun sojojin gwamnati. Kura ta lafa kuma an fara gudanar taron sulhu a kasar Uganda. Sai dai tun wannan lokacin sojojin 'yan tawayen ba su san takamamme alkiblar da aka sa a gaba ba."

Ita kuwa jaridar Frankfuter Allgemeine Zeitung labari ta buga game da boren da ake Afirka ta Kudu biyo bayan matakin da kamfanin Anglo Platinum ya dauka na rufe mahakarsa guda biyu a kasar.

"Bayan munanan yaje-yajen aikin da suka addabi bangaren hakan ma'adanai a Afirka ta Kudu a bara, yanzu kamfanin Anglo Platinum dake zama mafi girma a duniya wajen hakan farin karfe ya dau matakin rufe ma'aikatunsa guda biyu na lokaci mai tsawo, sannan zai sayar da wata mahakarsa guda. Wannan matakin zai janyo asarar guraben aikin mutane kimanin 14000. Tun farko dai kamfanin da kusan kashi 80 cikin 100 na sa mallakin kamfanin Anglo American ne mai hakan danyun kaya, ya ba da sanarwar tabka babar asara a shekarar cinikaiya da ta wuce. Ba dai abin mamaki ba ne kasancewa kamfanonin hakan ma'adanai a Afirka ta Kudu na fama da matsaloli kasancewa kamfanonin kera motoci a nahiyar Turai sun rage sayen kayakin aiki. Bugu da kari a Afirka ta Kudu a bara an fuskanci rikicin ma'aikata mafi muni tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata. Mutane fiye da 50 suka rasu sakamakon wadannan rigingimu."

Ba safai kasashen duniya ke nuna sha'awa da zaben gundumomi a Kenya ba, to amma inji jaridar Die Welt, idan zaben zai gudana ne a gundunmar Siaya, kauyen mahaifin shugaban Amirka Barack Obama, kuma dan uwansa ne ya tsaya takarar neman mukamin gwamna, to fa yana daukar hankali ba kadan ba. Malik Obama mai shekaru 54 wanda ya tashi a kauyen Nyang'oma Kogelo ya yanke wannan shawarar ce saboda nasarar da dan'uwansa ya samu ta ba shi kwarin guiwa kuma ta kasance wani kalubale a gare shi na taimaka wa al'ummar wannan yanki dake fama da tarin matsaloli na rigingimu, rashin aikin yi. A zaben na ranar 4 ga watan Maris Malik Obama zai fafata ne da Oburu Odinga dan'uwan Firaministan Kenya Raila Odinga.

Ministan ba da taimakon raya kasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel na shan suka dangane da wani shirin da ma'aikatarsa ta gabatar game da Afirka, inji mujallar Der Spiegel. Ta ce:

"Shirin wanda ke da niyar karfafa fahimta tsakanin Jamus da nahiyar Afirka zai ci euro miliyan takwas, sai dai ana saka ayar tambaya game da samun nasarar wannan shiri, domin ba a shigar da kasashen da abin ya shafa a cikin shirin ba."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu