′Yan tawayen ƙungiyar Seleka sun shiga birnin Bangui | Labarai | DW | 23.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawayen ƙungiyar Seleka sun shiga birnin Bangui

Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan tawayen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kutsa cikin babban birnin ƙasar Bangui.

Central African Republic President Francois Bozize (centre L, in blue) speaks to a crowd of supporters and anti-rebel protesters during an appeal for help, in Bangui December 27, 2012. Bozize on Thursday appealed for France and the United States to help push back rebels threatening his government and the capital, but Paris said its troops were only ready to protect French nationals. The exchanges came as regional African leaders tried to broker a ceasefire deal and as rebels said they had temporarily halted their advance on Bangui, the capital, to allow talks to take place. Picture taken December 27, 2012. REUTERS/Stringer (CENTRAL AFRICAN REPUBLIC - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)

Shugaban ƙasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Francois Bozize kewaye da askarawansa.

Shaidun gani da ido sun ce sojin gwamnati da dakarun 'yan tawaye sun gwabza fada gabannin shiga birnin, kazalika mazauna garuruwan da ke daura da birnin na Bangui sun ji harbe-harben manyan bindigogi da kuma tashin bama-bamai.

Kawo yanzu dai ba a tantance yawan yankunan da 'yan tawayen yanzu haka su ke rike da su ba tun bayan da su ka samu shiga birnin na Bangui a wannan Asabar din.

'Yan tawayen na Seleka dai wanda su ka lashi takobin hambarar da gwamnatin kasar sun sake daukar makamai a wannan makon ne bayan da su ka yi ikirarin cewar shugaban kasar Francois Bozize ya saba alkawurun da ya yi mu su na sanya wasu daga cikin dakarunsu a rundunar sojin kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman