1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin tashin hankali

January 14, 2021

Dakarun gwamnati a Jamhuiryar Afirka ta Tsakiya sun sanar da dakile 'yan tawayen da suka yi kokarin karbe iko da babban birnin kasar Bangui.

https://p.dw.com/p/3nunT
Zentralafrikanische Republik  Bangui - Camp Kassaï Camp Kassaï
Hoto: DW/H. Marboua

'Yan tawayen na Jamhuriyar Afirka ta Tasakiya sun kwashe watanni suna neman kutsawa Bangui babban birnin kasar, kafin su yi yunkurin cimma burinsu inda suka zo kusa da birnin, kilomita tara ne kawai ya hana su tsallakawa birnin. An kwashe sa'o'i ana barin-wuta kafin dakarun gwamnati su yi galabar hana 'yan tawayen shiga birnin na Bangui. Tun gabanin zaben da aka yi na watan Disambar da ya gabata kasashen duniya irinsu Rasha da Ruwanda suka taimaka wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da karin dakaru bayan na  MDD da ke kasar. Duk da cewa a lokacin sun yi nasarar hana juyin mulki, amma har ya zuwa yanzu zaman lafiya bai dawo kasar ba, duk kuma da cewa an yi zaben da ya sake ba shugaba mai ci nasara. Gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai ta ce tana iyakar kokarinta wurin ganin ta dawo da zaman lumana. Ta ce duk da kurarin da 'yan tawaye ke yi na cewa za su yi yunkurin juyin mulki amma da taimakon dakarun MINUSMA na MDD da kasashe irinsu Rasha da Ruwanda Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na ci gaba da samun galaba a kansu. Sai dai kuma ci gaba da wadannan hare-hare na nufin cewa yunkurin tattaunawa da sasanci tsakanin gwamnati da 'yan tawayen ya ruguje ke nan.