′Yan tawaye sun mika wuya a Kwango | Labarai | DW | 30.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawaye sun mika wuya a Kwango

An dai baiwa 'yan tawayen zuwa ranar biyu ga watan Janairu 2015 su mika wuya ko kuma su dandana kudarsu bayan gurfana a gaban kotun soji a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Rahotanni sun nunar da cewa kimanin 'yan tawaye dari da hamsin a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango sun mika wuya kafin cikar wa'adin shirin tsagaita wuta a ranar biyu ga watan Janairu na shekara mai zuwa.

Wannan dai nazuwa ne bayan da aka bukaci dakarun tawayen na Democratic Forces for the Liberation of Rwanda su ajiye makamai ko kuma su fuskanci hukuncin soji daga Majalisar Dinkin Duniya ko ma dakarun sojan kasar ta Kwango.

Wani babban jami'in ayyukan tallafi a yankin ya ce 'yan tawayen sun mika wuya ne ga mahukunta a lardin da ke kudanci da arewacin Kivu.

Wakilin DW a birnin Goma Jack Kahorha ya bada rahoton cewa wani Janar a bangaren na 'yan tawaye ya bayyana cewa zai ci gaba da jan hankalin 'yan tawayen da su ajiye makamai cikin gaggawa.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu