1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyi a kasar Siriya sun juya wa batun sulhu baya

Zulaiha Abubakar MNA
December 26, 2017

Kungiyoyin da ke adawa da gwamnatin Bashar al-Assad sun yi watsi da batun sulhun da kasar Rasha ta dauki aniyar yi.

https://p.dw.com/p/2pxyJ
Putin und Assad
Hoto: Getty Images/AFP/M. Klimentyev

'Yan tawaye da kuma kungiyoyin adawa a kasar Siriya sun ce ba za su laminci batun sulhun da kasar Rasha ke yunkurin yi tsakaninsu da shugaba Bashar Al-Assad ba, inda suka zargi Mosko da kin matsin lamba ga shugaba Assad a kan kawo karshen rikicin.

A wata sanarwa da kungiyoyin 'yan tawaye 40 da suka hada da jam'iyyun adawa suka fitar, sun bayyana tattaunawar sulhun da ake sa ran yi a watan Janeru da cewar wani kulli ne da zai maye shirin Majalisar Dinkin Duniya a kan sulhun, wanda bai haifar da wata nasara ba tun lokacin da aka fara a shekara ta 2014. Sun kuma kara da cewar Mosko ta umarce su da su jingine bukatarsu ta lallai sai shugaba Assad ya sauka daga mulki.

Za a shiga mataki na hudu a cigaba da sulhun tsakanin bangarorin da ke rigima da juna, sai dai har yanzu ba a tantance kungiyoyin da za su halarci tattaunawar ba, ko da yake kasar Turkiyya ta bada shawarar kada a gayyaci kungiyar 'yan tawaye ta Kurdawa wato PYD wacce ke rike da kashi 25 cikin 100 na yankin kasar ta Siriya, duk kuwa da cewar Rasha ta amince a gayyaci wannan kungiya.

A wani cigaban kuma na kara dankon alaka tsakanin kasashen biyu, Rasha na shirye-shiryen ba Siriya aron sansanin sojojin samanta da ke Siriya har na tsawon shekaru 49.