′Yan tawaye a kasar Yemen sun karbe ragamar jagoranci | Labarai | DW | 06.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawaye a kasar Yemen sun karbe ragamar jagoranci

'Yan tawaye a Yemen sun karbe mulkin kasar bayan sanarwar rusa majalisar dokoki

Rahotannin dake fitowa daga Yemen, na cewa mayakan tawayen Houtawa, sun karbe ikon jagoranci, inda tuni suka sanar da rusa majalisar dokokin kasar a yau Juma'a.

Matakin mayakan dai na zuwa ne kasa da makonni biyu da shugaban kasar Abd Rabu Mansour da mukarraban sa suka sanar da murabus din su.

Cikin wata sanarwa ta talabijin da aka watso daga fadar shugaban kasa dake birnin Sana'a, mayakan Houtawan sun ce za su kafa majalisar da zata zabi mambobin majalisar shugaban kasa da zasu jagoranci al'amuran kasar cikin wa'adin shekaru biyu da za a yi na riko a kasar.