1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda na cigaba da kai hari a kasar Mali

Zulaiha Abubakar MNA
February 10, 2018

Tashin nakiya ta hallaka mutane da dama da raunata wasu 18 a wasu garuruwa da ke yankin Mopti.

https://p.dw.com/p/2sSn1
Mali Anschlag in Gao
Hoto: Getty Images/AFP

Wasu fararen hula biyar sun rasa ransu yayin da mutane 18 suka samu munanan raunuka yayin da motar da suke ciki ta bi ta kan wata nakiya makwanni biyu bayan rasuwar mutane 26 matafiya sakamakon tashin nakiya a kasar Mali, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya sanar a ranar Asabar.

Tashin nakiyar ya faru ne a ranar Juma'a a kan hanyar dake tsakanin garuruwan Dera da Konna da ke yankin Mopti in da 'yan ta'adda suka matsantawa da kai wa hare-hare a cikin kwanakin nan.

A shekara ta 2013 rundunar sojojin kasar Faransa suka kai dauki kasar ta Mali inda kuma suka yi nasarar korar gungun 'yan ta'adda masu nasaba da kungiyar Al-Qaeda daga 'yankin arewacin kasar ta Mali.

Har yanzun dai ba kungiyar da ta dauki alhakin tashin nakiyar.