′Yan siyasa sun cimma yarjejeniya a Kwango | Siyasa | DW | 03.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan siyasa sun cimma yarjejeniya a Kwango

A Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango wasu 'yan adawar kasar sun yi mubayi'a ga yarjejeniyar kawo karshen rikicin siyasar kasar da zai bai wa Shugaba Kabila damar ci gaba da mulki har watan Febrairun shekarar 2018.

Kongo Präsident Joseph Kabila (picture-alliance/AP Photo/J. Bompengo)

Shugaban kasar Kwango Joseph Kabila

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ke ci gaba da aikin gyaran girgam din zabe na kasar. Wasu jiga-jigan 'yan adawar kasar 13 ne dukkaninsu mambobin kawancen jam'iyyun adawar kasar ta "Plate forme" da madugun 'yan adawar kasar ke jagoranta suka sanar da mika wuya ga yarjejeniyar da aka cimma. Wadannan 'yan adawa dai sun bada hadin kansu bayan da aka basu tabbacin cewa za a ba su mukamin firaministan gwamnatin riko da yarjejeniyar ta tanada.

Sai dai har yanzu wasu 'yan adawa na ci gaba da bijire wa wannan shiri na neman bai wa shugaba Kabila damar zarcewa kan mulki. Kuma Maitre Lotin Vangu kakakin kawancan CCT na masu yaki da tazarcen Shugaba Kabila ya bayyana takaicinsa da yadda wadannan 'yan adawa suka mika wuya ga shirin gwamnatin.

Demokratische Republik Kongo Unruhen (Picture-Alliance/AP Photo/J. Bompengo)

An dai fuskanci rigingimu a kasar saboda matakin Kabila na neman yin tazarce

A daidai lokacin da ake ci gaba da wannan cece-kuce, daga nata bangare hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Jamhuriyar Demokradiyyar kwango ta sanar a ranar 31 ga watan Oktoban da ya gabata cewa ta kammala aikin sabunta girgam din masu zabe na kasar Ta kuma sha alwashin soma aikin rarraba kayan zabe a karshen watan Janairun sabuwar shekara. Idan dai har duk wadannan ayyukan suka kasance a cikin wa'adin da hukumar zaben ta tsaida za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na farko a ranar 29 ga watan Afrilun shekara ta 2018.

Sai dai wasu jam'iyyun adawar da ma kungiyoyin fararen hula na kasar sun sha alwashin bijire wa wannan zabe. Amma Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da shirin aiko da wata tawagarta a kasar daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Nuwamba domin tattaunawa da bangarorin da ke hamayya da juna a kasar da nufin ganin an tsaida wani jadawali da zai ba da damar gudanar da zaben a cikin lokaci mafi kusa a nan gaba.

Sauti da bidiyo akan labarin