′Yan sandan Spain sun hallaka ′yan ta′adda biyar | Labarai | DW | 18.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sandan Spain sun hallaka 'yan ta'adda biyar

Jami'an tsaron Spain sun karfafa matakan tsaron neman mutumin da ya kutsa da babbar mota tare da hallaka mutane 13 yayin da wasu fiya da 100 suka jikata.

Jami'an tsaron kasar Spain sun hallaka 'yan ta'adda guda biyar wadanda aka samu rahoton suna shirin kai hari kan mutane a garin Cambrils da ke kunshi da masu yawon shakatawa, lamarin da yake zuwa sa'o'i bayan irin wannan hari da aka kai da babbar mota, ya kai ga mutuwar mutane 13 yayin da wasu fiye da 100 suka samu raunika a garin Barcelona.

Shi dai birnin na Cambrils yana da nisan kilo-mita 120 kudancin Barcelona. Akwai mutane shida da suka jikata gami da dan-sanda daya lokacin farmakin na garin Cambrils. Game da harin na Barcelona jami'an tsaro sun cafke mutane biyu, akwai rahoton daya daga cikin wadanda ake zargi an bindige shi har lahira, amma ana ci gaba da neman matukin babbar motar da ya kutsa cikin mutane.

Tuni Firaminista Mariano Rajoy na kasar ta Spain ya katse hutun da yake yi domin ziyarar gani da ido a birnin na Barcelona kuma tuni ya yi tir da harin. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana cikin shugabannin kasashen duniya da suka mayar da martani wajen n una takaici bisa harin na kasar Spain.