′Yan sandan Masar sun fafata da fararen hula | Labarai | DW | 16.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sandan Masar sun fafata da fararen hula

A Masar, jami'an 'yan sanda 31 ne suka ji rauni a fito na fito da mazauna gabar Tsibirin da ke birnin Cairo a yayin rusa gidajen da ba a gina su a kan ka'ida ba.

Mazauna tsibirin sun yi wa 'yan sandan jifa da duwatsu abin da ya harzika 'yan sandan kai martaninn kariya da hayaki mai sa hawaye. A yanzu dai rahotanni daga cibiyoyin kiwon lafiya na cewar guda daga cikin masu karban jinya ya rasu. Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da jami'an tsaron kasar suka tabbatar da kashe wasu mutane tara da ake zargi da ayyukan ta'addanci a yankin Sinai, tare da lalata motoci 15 da ake safarar muggan makamai ta kan iyakar kasar da Libiya.