1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan kasar Denmak sun kama mutane biyu

Suleiman BabayoFebruary 16, 2015

Mahukuntan kasar Denmak sun kaddamar da bincike kan wasu hare-hare biyu da aka kai babban birnin kasar

https://p.dw.com/p/1EcSD
Dänemark Anschläge in Kopenhagen
Hoto: Reuters/L. Foeger

'Yan sandan kasar Denmak sun kama mutane biyu da ake zargin da taimakon dan bindiga dadin da ya kai hare-hare a Copenhagen babban birnin kasar.

'Yan sanda sun hallaka maharin lokacin musanyen wuta. Hare-hare na birnin Copenhagen an kai wajen shan gahawa da ake muhawara kan 'yancin fadin albarkacin baki, da kuma wata cibiyar Yahudawa. Shugaban kasar Faransa Francois Hollande da yake mayar da martani kan hare-haren na kasar ta Denmak, ya tabbatar da cewa ana maraba da Yahudawa a Faransa da sauran kasashen Turai, kuma babu wanda ya isa ya kore su.