′Yan sandan Jamus za su tsananta binciken iyakoki | Labarai | DW | 30.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sandan Jamus za su tsananta binciken iyakoki

Ministan cikin gidan Jamus Horst Seehofe yace ‘yan sandan kasar za su tsananta binciken ba zata a kan iyakoki domin dakile shigowar 'yan gudun hijira daga kasashen da ba na kungiya EU ba.

Wannan mataki a cewar ministan cikin gidan Jamus Horst Seehofe na da nufin tsaurara tasaro a kan iyakoki domin hana kwarararowar ‘yan gudun hijira da ‘yan cirani daga kasashen da ba na kungiyar tarayyar Turai. 
 
Tun da farko Seehofer ya sanar da tsawaita zaman jami’an tsaron iyakoki a kan iyakar Jamus da Austria har zuwa lokacin bazara na shekarar 2020.

Wani mai Magana da ywun ma’aikatar cikin gidan yace ‘yan sanda sun cigaba da gano mutane masu yawa da ke shigowa ta iyakokin kasar ba bias ka’ida ba.

Rahotanni sun ce kawo yanzu yan sanda sun kama bakin haure kimanin 38,000