′Yan sanda sun tarwatsa gangamin adawa da zaben Aljeriya | Labarai | DW | 12.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda sun tarwatsa gangamin adawa da zaben Aljeriya

An fuskanci karancin masu kada kuri'a a zaben shugaban kasar Aljeriya yayin da jami'an tsaro suka tarwatsa dandazon masu zanga-zanga da ke adawa da zaben.

'Yan sadan sun watsar da taron masu zanga-zanga da suka fara taruwa a babban wurin taro da masu boren ke haduwa domin adawa da gwamnati. 

'Yan takara biyar ke fafatawa a zaben domin maye gurbin tsohon shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, sai dai 'yan kasar na Allah wadai da daukacin 'yan takara a zaben, inda suke alakantasu da tsohon shugaban.