Yan sanda a Zimbabwe sunyi barazanar tarwatsa taron yan adawa | Labarai | DW | 13.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan sanda a Zimbabwe sunyi barazanar tarwatsa taron yan adawa

Yan sanda a kasar Zimbabwe sunyi barazanar hana wani taron adduoi da coci coci da kungiyoyin adawa suna masu cewa yin hakan karya dokar hana gangamin siyasa ne a kasar.

Kungiyoyin adawa sunce sun shirya gudanar da adduopin ne na tsawon saoi 4 a birnin Bulawayo a gobe asabar idan Allah ya kai mu.

Yan sanda sun tarwatsa addoui na baya da aka shirya a ranar 11 ga watan maris a birnin harare a inda suka lallasa wasu yan adawa.

Mai magana da yawun yan sanda Wayne Bvudzijena yace bincike da suka gudanar ya nuna cewa taron wani gangami ne na siyasa ba adduoi ba wanda tilas sai sun bada sanarwar kwanaki 4 kafin gudanar da iata.