′Yan sanda a New York sun bakunci lahira | Labarai | DW | 21.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda a New York sun bakunci lahira

Shugaba Barack Obama ya bayyana Allah wadai da kisan wasu 'yan sanda biyu a birnin New York na Amirka kisan da ya bayyana da cewa babu wani dalili da zai sa a kaita shi.

A jiya Asabar ne dai da tsakar rana kiri-kiri aka aikata wannan kisa na 'yan sanda a kasar ta Amirka.

Obama ya ce ba hujja ta aikata shi ba dan komai ba sai dan kasancewar 'yan sanda sun sadaukar da rayukansu ne domin ba da kariya ga al'umma da dukiyoyinsu saboda haka sun cancanci mutuntawa da godiya.

A cewar mahukunta a Amirkar kafin aikata kisan dan bindigar ya bayyana a shafin intanet cewa zai hallaka wasu aladu guda biyu a matsayin fansa ga kisan Eric Garner wani mutum da 'yan sanda suka yi wa shaka da tayi sanadin mutuwarsa bayan ya fada musu cewa ba ya iya numfashi.

Daga baya ma dai dan bindigar ya halaka kansa bayan ya aikata kisan.

Shugaba Obama dai ya bukaci Amirkawa su guji daukar doka a hannu da furta kalaman batanci, ya kamata su mayar da hankali wajen addu'a da kalaman da za su kawo kwanciyar hankali da nuna tausayawa ga iyalan wadanda 'yan sanda suka kashe a Amirka ba tare da an cajesu da laifi ba.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo