′Yan sanda a Australiya sun cafke wasu ′yan ta′adda | Labarai | DW | 18.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda a Australiya sun cafke wasu 'yan ta'adda

Hukumomin tsaro sun ce sun murƙushe wani yunƙurin kai hari na ta'addanci da Ƙungiyar masu jahadi ta IS ta kitsa kai wa wanda ya ci tura.

A wani harin da 'yan sanda suka kai a biranen Sydney da Brisbane sun kame mutane guda 15 waɗanda ake zargi da hannu. Gwamnatin ta Australiya ta baza 'yan sanda 800 domin ƙaddamar da wannan aiki na yaƙi da ta'addanci.

Gidan telbijan na ABC na Australiyan ya ce maharan sun shirya sace wani farar hula a bazata a Sidney wanda suka so su hile masa kai.