'Yan sanda 1,500 a birnin Kwalan saboda tsaro | Labarai | DW | 12.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda 1,500 a birnin Kwalan saboda tsaro

Za dai a rarraba 'yan sanda wuri-wuri da suka hadar da babbar tashar jiragen kasa da ke a birnin dan kaucewa lagudar 'yan mata da aka samu a bara, zargin da ake wa wasu matasa daga Arewacin Afirka da Larabawa.

Kimanin 'yan sanda 1,500 ne za a jibge a birnin Kwalan da ke a Yammacin kasar Jamus a wani bangare na shirye-shiryen bikin sabuwar shekara, sannan za a makala na'urorin daukar bayanai na kai kawo jama'a a dandalin da ke tsakiyar birnin dan kaucewa abin da ya faru a shekarar bara inda wasu matasa suka aikata abubuwan cin zarafi ga mata kamar yadda Juergen Mathies shugaban 'yan sanda a birnin ya bayyana.

Cikin matakan da za a dauka dai sun hadar da jibge jami'an rukuni-rukuni uku dauke da misalin 'yan sanda 300 da za a a ajiye a kusa da babbar majami'ar nan ta Kwalan cathedral kamar yadda Mathies a taron manema labarai, wanda mahalartansa har da Magajiyar garin birnin na Kwalan Henriette Reker da babban jami'in 'yan sanda su ka halarta.