′Yan Najeriya na ƙara rungumar kuɗin Dala maimakon Naira | Siyasa | DW | 22.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan Najeriya na ƙara rungumar kuɗin Dala maimakon Naira

Mahukunta da masu tsare-tsaren tattalin arziki na nuna matuƙar damuwa game da ƙaruwar amfani da Dalar Amurka a hada-hadar kasuwancin ƙasar.

Ƙaruwar amfani da takardar kuɗi ta Dala a hada-hadar kasuwanci a Najeriya na zama abin damuwa ga mahukunta da ma masu tsare-tsaren tattalin arziki saboda irin ƙaluballen da hakan ke da shi ga al'umma Najeriyar da ma tattalin arzikin ƙasar kansa.

Takardar kuɗi ta Naira dai ita ce halattacciya wacce a Najeriyar aka amince da a yi amfani da ita wajen hada-hada ta yau da kullum, to sai dai sannu a hankali takardar kuɗin dalar Amurka na maye gurbin ta Naira a hada-hadar cinikaiyya a fannoni da dama a Najeriyar abinda ya sanya nuna damuwar yadda dalar ke zama takardar kuɗin ta biyu da ake hada-hada da ita a Najeriya ba ya ga Naira.

Dala ta mamaye Naira a wasu hada-hada a Najeriya

Domin kuwa daga biyan kuɗi a wasu makarantu na 'ya'yan masu hannu da shuni zuwa ga asibitoci masu zaman kansu da ma kuɗin wasu otel-otel duka ana biya ne da takardar kuɗin dalar Amurka maimakon Naira, abinda sannu a hankali sai ƙaruwa yake yi zuwa ga hada-hadar.

Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos

Faɗuwar darajar Naira ta sa wasu 'yan Najeriya ba sa sha'awar ajiye ta

Ƙwararru na danganta wannan lamari da dalilan faɗuwar darajar takardar kuɗin Najeriyar ta Naira da ke haifar da wahalhalu ga al'ummar ƙasar. To sai dai ga Dr. Hussaini Tukur ƙwararre a fannin tsare-tsare da ci gaban ƙasa da ke jami'ar jihar Nasarawa ya ce matsalar ta wuce yadda ake tunane?

"Watau na farko dai za'a raunana tattalin arzikinku da ma'amalolinku, alal misali idan za'a zo cikin kasarku a sayi abu a cikin dala ko kuma a biya kuɗin hotel ko a biya albashi to darajar kuɗinku ta sauka, wannan ya na ɗaya daga cikin abinda ya jawo yanzu Naira ɗaya, kwabo hamsin, Naira biyar, Naira goma, Naira ashirin ba su da daraja. Kuma a tsare-tsaren ƙasa duk lokacin da ka yi tsari da dala, idan ta tashi tsarinka ya karye, a duk lokacin da dalla ta karye tsarinka ya karye, za ka zama kullum kana shirye-shiryen ya za'a gyara tsarin, maimakon ya za'a yi a tafiyar da ci gaban ƙasa kullum ya za'a yi a gyara tsarin."

Amfani da Dala illa ce ga tattalin arzikin ƙasa

Koda yake gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwarta a kan lamarin saboda sanin illar da ke tattare da hakan to sai dai maimakon samun sauyi abin sai gaba yake, domin bayanai sun nuna yadda 'yan Najeriya da dama a yanzu suka gwammace adana 'yan kuɗaɗensu a kuɗaɗen ƙasashen waje musamman ma dai dalar Amurka maimakon Naira.

Zentralbank von Nigeria

Babban bankin Najeriya ya sha alwashin ɗaukar matakai don maido da darajar Naira

Ko me ke haifar da wannan sauyi a tsakanin al'ummar ƙasar? Malam Yusha'u Aliyu masanin tattalin arziki ne da ke a Abuja Najeriya.

"Watau yadda tattalin arzikin ƙasar ne ya kai, kuɗin ƙasar darajarsa na ta zubewa da ƙarfinsa bai da tasirin da zai riƙe kowane irin ɗan kasuwa saboda yarda. Saboda dalilin da yasa ake riƙe kuɗi na ɗaya saboda harkar kasuwanci na biyu saboda aje kuɗi don darajarsa na uku don tunanin yadda kuɗin zai taimaka ma tattalin arzikinka kai kanka, watau ya ɗaukaka. Da in ka tuna ai kuɗin ƙasar ana karɓanshi a wasu ƙasashe nusamman Saudi Arabiya da wasu na duniya, amma yanzu ba'a karɓan kuɗin, saboda haka rashin karɓan shi a waje ya dawo cikin gida."

Gwamnatin ta sha alwashin ɗaukar mataki

Tuni gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sunusi dai ya ce gwamnatin Najeriyar ta fara ɗaukan matakan da suka dace da za su iya sauya lamarin, waɗanda suka hada da yunƙurin dakatar da amfani da kuɗi kai tsaye wajen sayarwa masu musayar kudaɗen ƙasashen waje dalar Amurkan.

Abin jira a gani shine ko wannan zai iya yin tasiri a ƙasar da shekaru da dama an sakewa jama'a suna farautar dalar Amurka a yanayin da ke haifar da haihawar farashin kaya da koma bayan tattalin arziki ga al'ummar ƙasar, waɗanda hukumar ƙididigar jama'a ta bayyana kashi 70 cikin 100 na yawansu su na fama da talauci.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin