′Yan mata miliyan 12 ke auren wuri | Labarai | DW | 06.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan mata miliyan 12 ke auren wuri

Asusun kula da kananan yara na Unicef ya sanar da cewar ana cigaba da aurar da 'ya'ya mata 'yan kasa da shekaru 18 duk shekara a wata kididdiga da hukumar ta fitar a wannan Talata.

Sanarwar ta bayyana cewar an samu cigaba da kashi 15 in aka kwatanta da shekarun baya da ake aurar da yarinya guda daga cikin hudu, sai dai duk da hakan UNICEF daga nan sai ya yi jan hankali akan in aka cigaba da aurar da 'yan mata masu kananan shekaru, to kuwa 'yan mata sama da miliyan 150 a fadin duniya za su yi aure kafin su kai shekaru 18, daga yanzu zuwa shekara ta 2030. A halin yanzu kididdiga ta nuna cewar sama da matan aure 650 a duniya, an aurar da su ne tun suna kananan yara.

A wani cigaban kuma Sashen Muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya, ya shirya tsaf don kawo karshen auren wuri kafin shekara ta 2030.