1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Maroko na adawa da daure el-Zafzafy

Mahmud Yaya Azare MAB
June 28, 2018

Hukuncin da kotu ta yanke wa madugun boren neman sauyi ya jawo barkewar zanga-zangar a Maroko. Daurin shekaru 20 aka yanke wa Nasser Zafzafy, yayin da magoya bayansa 49 suka fuskanci daurin shekaru 2 zuwa15 a gidan yari.

https://p.dw.com/p/30TNI
Marokko | Proteste in Rabat
Hoto: picture-alliance/abaca/J. Morchidi

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da daure madugun kawo sauyi ga tsarin tattali da zamantakewar kasar ta Maroko Nasser Zafzafi mai shekaru 39 da haihuwa. Tun a watan Mayu na shekarar 2017 ne ake tsareshi kan jagorantar zanga-zangar neman bin kadin Munsin Fikri, wani mai tallan kifi da ya mutu a yayin da 'yan sanda suka tattarashi, shi da teburinsa suka jefa cikin motar shara.

Alkalan da suka yanke wannan hukuncin da wasu ke ganin yayi matukar tsauri sun zargi Zafzafi da takwarorinsa da tarin laifufukan da suka hada da tada yamutsin da ya kai ga rasa rayukan 'yan kasa, da lalata kadarorin gwamnati gami da yi wa jami'an tsaro kutse, kai har ma da kitsa makarkashiyar kifar da gwamnati. Wadannan laifufukan dai, lauyan gwamnati Muhammad Husaini Krout ya ce sun kai ga hukuncin kisa.

Marokko Proteste
A shekarar da ta gabata ne hukumomin Maroko suka kama Nasser ZafzayHoto: picture-alliance/AP Photo/A. Mohamed

Ya ce "An yi sassauci a wannan hukuncin domin idan da za mu yi la'akari da nasfsosin doka, da hukuncin kisa za aiyanke musu saboda girman laifuffukan da yawan wadanda suka cutu da kuma maimaita laifufuukan da suka ta yi.”

Sai dai tsohon ministan ma'aikatar kare hakkin bil Adama ta kasar Muhammad Zayyan na gani cewa irin wannan shari'ar ba abin da take tsinanawa ga kasa kan banda karin tashin-tashina.

Ya ce   "Na ji takaicin yadda aka rarraba hukuncin daurin kimanin shekaru dari uku kan masu fafutuka hamsin. Wannan ba zai haifar wa kasar nan da mai ido ba. A maimakon ya kara wa gwamnati farin jinni, zai zubar da kimar tsarin shari'a ne, domin kundin tsarin mulki ya ba wa y'an kasa y'ancin zanga-zangar lumana don neman sauye -sauye, ko da kuwa abun zai kai ga neman a sauke gwamnati ne.”

Marokko Protest von Frauen in Rif
Mata na daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zanga a biranen MarokoHoto: Mohamed Amahjik

Duk da cewa lawyoyin wadanda aka yanke wa hukuncin na da damar daukaka kara, sai dai kamar yadda Ahmad El-Hayeej shugaban hukumar kare hakkin bil Adama na kasar ke cewa bai zatan za ta canja zani:

  "Wannan hukuncin yana kara tabbatar mana da cewa matakan fafutuka ne kadai zas u iya 'yantarmu a kasar nan, domin tsarin shari'a ya riga ya zama tamkar y'ar tsana a hannun gwamnati, ita ke juyashi yadda take so.”