Mali: Zaben shugaban kasa zagaye na biyu
August 12, 2018Talla
Sai dai ana iya cewa zaben ba zai haifar da tururuwar jama'a ba, domin kuwa tuni da dama ke ganin cewaR an san wanda zai lashe zaben musamman ma Shugaban mai ci Ibrahim Boubacar Keita, wanda ya zo na farko a zagayen farko da babbar tazara, sannan abokin hamayyarsa dan takara na bangaran adawa Soumaïla Cissé, bai samon goyon bayan sauran manyan jam'iyyun kasar na bangaran adawa ba, inda suka kira magoya bayansu da kowa ya zabi son ransa. A ranar Asabar dai jajibirin wannan zabe jami'an tsaron farin kaya na Mali sun kama wasu mutane guda uku da ake zargi da shirya ayyukan ta'addanci a Bamako babban birnin kasar.