′Yan Malesiya na boren kin jinin gwamnati | NRS-Import | DW | 19.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

'Yan Malesiya na boren kin jinin gwamnati

Kungiyoyin fararen hula sun zargi Firaminista Najib Razak na Malesiya da karkatar da dukiyar kasa, saboda haka suka shirya zanga-zanga domin tilasta masa sauka daga mulki.

Dubban 'yan Malesiya sun gudanar da zanga-zanga a Kuala Lumpur babban birnin kasar domin tilasta wa Firaminista Najib Razak sauka daga mulki sakamakon zarginsa da suke yi da sama da fadi da dukiyar kasa. Gamayyar kungiyoyin fararen hula ta Bersih ce ta bukaci jama'a su sanya tufafi ruwan goro tare da fantsama kan tituna, domin neman kawo karshen mulkin Razak tare da gurfanar da shi gaban kuliya. Tana ganin cewar yana da hannu dumu-dumu a badakalar kudi da ta mamaye wani kamfanin gwamnati da Firaminista Najib Razak ya kafa shekaru bakwai da suka gabata, amma kuma bashi yai mata katutu.

Gabanin zanga-zangar dai hukumomin Malesiya sun sa an kama wasu shugabannin kungiyoyin fararen hula, lamarin da ake ganin cewar zai iya ruru wutar rikicin. Jami'an kwantar da tarzoma sun yi wa birnin na Kuala Lumpur kawanya. Sai dai cikin wata hira da ya yi da tashar rediyo ta gwamnati, Firaminista Najib Razak ya zargi masu zanga-zangar da neman hambarar da shi ta hanyar da bata dace ba.