′Yan majalisun Faransa na fatan samun kasar Falesdinu | Labarai | DW | 26.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan majalisun Faransa na fatan samun kasar Falesdinu

A wata wasika da suka aike wa shugaban kasar Faransa François Hollande, 'yan majalisun dokokin kasar 154 sun nemi da shugaban kasar da ya amince da Falesdinu a matsayin kasa ba tare da bata lokaci ba.

Frankreich Präsident Francois Hollande (Reuters/Ph. Wojazer)

Shugaban kasar Faransa Fransoi Hollande

Cikin wasikar dai 'yan majalisun na kasar Faransa sun ce, ya kamata kasar Faransa ta nuna kanta ta hanyar fita daga cikin wannan hali na rashin tabbas domin ta sanar wa duniya da sunan inci, cewa al'ummar Falesdinawa sun cancanci samun ta su kasa. Kuma hakan zai kasance yin biyayya ga dokokin kasa da kasa, da kuma tsaron lafiyan kasar Isra'ila.

Don haka suka yi kira ga Shugaba Hollande da ya nuna yana da karfin yin hakan, ba tare da ya bari wannan dama mai cikeken tarihi ta kubce masa ba. Akasarin 'yan majalisun na bangaran masu mulki da ma na adawa dun sun bi wannan sahu, inda suka rattaba hannu kan wannan bukata ta ganin Falesdinu ta zamana kasa mai cikekken iko.