1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisar Nijar sun ziyarci kasar Chadi

Abdourazak Garba Baba'aniMarch 20, 2015

Tawagar 'yan majalisar dokokin jamhuriyar Nijar ta ziyarci kasar Chadi don inganta dabarun arziki da kyautata huldar tsaro

https://p.dw.com/p/1EunS
Hajiya Hauwa Abdu
Hoto: DW/Mahamman Kanta

Bayan wata ziyarar da shugaban kasar Nijar Mouhamadou Issoufou ya kai kasar Chadi makwanni biyun da suka gabata, wata tawagar 'yan majalisar kasar ta ziyarci Chadin itama don neman hada dabaru da kuma kwarewar Chadin a harkokin man fetur don iya ware kudade daga rarar man saboda amfanin na baya masu tasowa.

Jagoran tawagar 'yan majalisar kasar ta Nijar lokacin ziyarar, Lamido Moumini Harouna ya jawo hankali al'umomin kasashen biyu kan bukatar yin taka tsantsa da rigimar nan ta yaki da kungiyar Boko Haram da kasashen ke ciki yanzu, inda ya bukaci musamman sojojin kasashen su guji cin zarafin fararen hula.

Lamido Moumini Harouna, ya kuma ce yakin da ake ciki da Boko Haram, yaki ne da ya shafi dukkanin kasashen da ke fuskantar barazana daga wannan kungiya.