′Yan Kwango na ban kwana da Tshisekedi | Labarai | DW | 31.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Kwango na ban kwana da Tshisekedi

Dubban 'yan kasar Kwango na zuwa filin wasa na babban birnin kasar don yin ban kwana da gawar tsohon jagoran adawa Etienne Tshisekedi.

Tshisekedi dan shekaru 84 ya rasu a Beljiyam shekaru biyu da suka gabata amma mahukunta a wancan lokaci suka hana a dawo da gawarsa saboda fargabar kada hakan ya tada rikici a kasar. Sai dai an samu sauyi bayan da dan Tshisekedi ya yi nasarar zama shugaban kasa a zaben da aka yi a watan Janairu.

Tsohon shugaban kasar ta Kwango dai Joseph Kabila ya sauka daga kujerarsa bayan shekaru 18 yana kan karagar mulki. Bayan nasarar dan na Tshisekedi ne dai wato Felix Tshisekedi ya sha alwashi na dawo da gawar mahaifinsa don a binne ta a kasar ta Kwango.