′Yan Kamaru sun tsere zuwa Najeriya | Labarai | DW | 28.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Kamaru sun tsere zuwa Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce sama da mutane dubu biyu ne daga kudancin kasar Kamaru suka tsere zuwa Najeriya, sakamakon rikici da ya shafi bangaren kasar da ke amfani da Ingilishi.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ta ce sama da mutane dubu biyu ne daga kudancin kasar Kamaru suka tsere zuwa Najeriya cikin makonni biyun da suka gabata, sakamakon rikici da ya shafi bangaren kasar da ke amfani da Ingilishi. Ana dai farbagar cewa kasar ta Kamaru wadda galibin al'umarta ke amfani da harshen Faransanci na iya shiga wata doguwar rudani, bayan wasu sojojin kasar sun kashe mutane akalla takwas a yankunan kasar masu amfani da Ingilishi a farkon wannan watan.

A cewar wani babban kwamishinan da ke kula da 'yan hijira Antonio Jose Canhandula, a halin da ake ciki, sun samar da wani tsarin da zai iya kula da 'yan kasar ta Kamaru dubu 40 da ka iya tserewa daga kasar. Rikicin harshe a Kamarun dai batu ne da ya samo tushe bayan yakin duniya na farko, lokacin da gamayyar kasashe suka raba Kamarun ga Faransa da kuma turawan Ingila.