1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafin 'yan Kamaru ga yankin Ingilishi

Gazali Abdou Tasawa
July 24, 2018

A Kamaru, wata daya bayan da shugaban kasar ya yi shelar neman agajin kudi daga 'yan kasar domin agaza wa mutanen da rikici ya ritsa da su a yankin da ake Ingilishi, an yi nasarar tattara sama da miliyan dubu na Cefa.

https://p.dw.com/p/3200z
Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Kamaru: Zanga-zanga a yankin IngilishiHoto: Getty Images/AFP

Wata daya bayan kiran da Shugaba Paul Biya ya yi ga 'yan kasarsa, kusan illahirin yankunan kasar ta Kamaru ne suka dage wajen kawo tasu gudunmawa domin taimaka wa dubunnan mutanen yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi na kasar ta Kamaru mai fama da rikicin 'yan awaren Ambazoniya wadanda suka tsinci kansu a cikin halin ha'ula'i.

Al'ummar birnin Douala da kewaye sun taimaka da kudi sama da miliyan 36 na cefa, na yankunan gabar ruwa sun samar da miliyan 177, jihohin tsakiya sun tattaro miliyan 152 na kudancin kasar  sun hado miliyan 120 na Cefa, jihohin yankin yammacin kasar sun kambado miliyan 430 na Cefa a yayin da al'ummar yankin Arewa mai nisa ta taimako da kudi miliyan 192 na Cefa, kana Adamaoua ta bayar da gudunmawar miliyan 48 na Cefa. Kuma 'yan kasar ta Kamaru ka dauka tun daga kungiyoyin fararan hula zuwa 'yan siyasa na bangaren adawa balantana masu mulki kowa ya yaba da wannan kokari da 'yan kasa suka yi kamar dai yadda Florence Aimee Titcho sakataren harkokin kudi a jam'iyyar Manidem daya daga cikin jam'iyyun da suka bayar da tasu gudunmawa ke cewa:

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Jana'izar sojojin Kamaru da aka kashe a yankin IngilishiHoto: Getty Images/AFP

"Shiri ne mai kyau domin akwai jama'armu na yankin Arewa maso Yamma da na Kudu maso yammacin kasar da ke cikin wahala, inda ta kai ba sa iya samun abinci kuma ba sa iya kaura daga wurin da suke yanzu. Dan haka wannan ai shiri ne na taimakon 'yan uwanmu na wadannan yankuna biyu. Kuma haka ya kamata, domin bai dace ce a ce sai Kamaru ta jira taimako daga wasu kasashen ketare ba"

Sai dai wasu bayanai sun nunar da cewa ba illahirin kudin da aka tattara ba ne ya shigo baitilmali ya zuwa yanzu, a yayin da wasu tarin kadarorin na miliyoyin kudade da aka tattara ke can jibge a runbunan ajiyar cimaka na rundunar sojoji masu aikin gine-gine ta kasa da ke a birnin Douala. Wannan ce ma ta sanya wasu 'yan kasar ta Kamaru soma nuna shakkunsu a game da makomar wannan dukiya a aka tara da sunan mabukatan yankin Inglishin. Don Romain Tchato na kungiyar direbobi masu jigilar jama'a da dukiyoyinsu zuwa yankin na masu magana da Ingilishi ko Anglophone na daga cikin masu irin wannan damuwa:

Kamerun Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul BiyaHoto: picture alliance/abaca/E. Blondet

"Wannan kudi da ake tattarawa wai ma mi takamaimai ake son yi da su. Ni dai na san ba dan a  biya wa yaran kudin makaranta ne ba, domin iyalai na zaune ne a cikin dazuka. Za a iske su ne a dajin a raba masu kudin ko abinci? Wannan duk tambayoyi ne da ba su da amsa yanzu, dan haka ya kamata a zauna a tattauna"

Ko ma dai mi ake ciki, a yanzu 'yan kasar ta kamaru da dama ne ke ganin abu mafi a'ala da ya kamata Shugaba Biya ya mayar da hankali kansa shi ne hawa teburin sulhu da 'yan awaren yankin na Ambazoniya domin gano bakin zaren warware matsalar ta yadda kasar ta Kamaru za ta ci gaba a zama kasa daya al'umma daya.