′Yan kaka gida na Afurka a Jamus | Siyasa | DW | 31.08.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan kaka gida na Afurka a Jamus

Ko da yake akwai 'yan Afurka da dama da suka dade da zama a nan Jamus, amma har yau da yawa daga cikinsu ba su saki jiki domin cude-ni-in-cude-ka da takwarorinsu Jamusawa ba

Tun a misalin shekaru 25 da suka wuce ne wata ‚yar kasar Eritriya da ake kira Berhane da yiwo kaura tare da wasu daga cikin danginta zuwa nan Jamus, amma kamar yadda ta nunar, har yau ba ta saki jiki domin zama na dindindin a kasar ba. A wancan lokaci ita Berhane tana da shekaru biyar da haifuwa. Da farkon fari iyayenta, wadanda tsaffin dakarun yakin neman ‚yancin kan Eritriya ne daga kasar Habasha, sun yi kaura ne zuwa Sudan sannan daga bisani suka karaso zuwa Jamus. Ta ce a cikin watan desamba na 1979 suka iso Hannover a daidai lokacin sanyin hunturu mai radadin gaske. A cikin dan gajeren lokaci ita da ‚yan uwanta suka koyi harshen Jamusanci suka kuma kulla kawance da dama. Amma duk da haka har yau ji take yi tamkar ita bakuwa ce a kasar nan, alhali kuwa tana rike ne da takardun shaida da fasfon Jamus. Abu daya da take madalla da shi shi ne kasancewar tun bayan da ta amince da zama cikakkiyar ‚yar kasa al’amura suka sawwaka a gare ta, kamar dai neman muhallin zama ko aikin yi da sauran dangantaka da mahukunta. Amma a baya ga haka ba zata iya hakikance cewar ita cikakkiyar ‚yar kasar Jamus ba ce. Domin kuwa galibi, mutane a nan kasar sun fi ba da la’akari da launin fatar mutum kuma a saboda haka wata takarda ta shaida bata da wata sahihiyar ma’ana a gare su. Berhane ta kara da nuni da cewar a wani lokaci ta kan zauna tana mai kewar gida Eritriya tare da fatan cewar watan-wata-rana zata samu ikon nuna wa ‚ya’yanta kasarsu ta asali. A ganinta ba zata fuskanci wata wahala ba idan ta koma gida saboda tana jin yarensu kuma mutane zasu karbe ta da hannu biyu-biyu. A shekarar 1993 ne kasar Eritriya ta samu ikon cin gashin kanta daga Habasha, amma ita Berhane har yau ba ta samu ikon kai ziyara domin saduwa da sauran danginta dake can Asmara, fadar mulkin Eritriya ba, ko da yake, kamar yadda ta nunar, suna tuntubar juna akai-akwai. An samu cikakken hadin kai tsakanin ‚yan usulin kasar Eritriya dake kaka-gida a nan Jamus domin kare makomar yare da al’adunsu tare da ba da gudummawa iya mustada’a a fafutukar neman ‚yancin kan kasarsu. Amma fa wani abin da ya taimaka Berhane da sauran ‚yan uwanta suka samu saukin tafiyar da al’amuran rayuwarsu a nan kasar tun da farkon fari shi ne cikakken hadin kai da goyan baya da suka samu daga wasu ma’aurata dattawa dake makobtaka da su, wadanda suka dauki yaran tamkar jikokinsu. A baya ga haka cude-ni-in-cude-ka da tayi tare da sauran yara tsattsan baki da Jamusawa ya taimaka wajen saukake mata al’amuran rayuwa ta yadda ba ta taikacin kasancewarta Bajamushiya, amma ‚yar usulin Eritriya. Ta ce a halin yanzu Jamus na da fuskoki da dama kuma ita kanta tana daya daga cikin wadannan fuskoki.