′Yan jihadi sun kame gidan Rediyo a Libiya | Labarai | DW | 13.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan jihadi sun kame gidan Rediyo a Libiya

Wasu da suke kiran kansu 'yan jihadi na kungiyar IS a Libiya, sun kame wani gidan rediyo a birnin Syrte da ke nisan km 500 da Tripoli tare da kafa sansaninsu a birnin.

Wasu hotuna da 'yan jihadin suka wallafa ta wani shafin Internet, sun nuno mutane dauke da makammai a cikin gidan radiyon bisa teburin da ake watsa shirye-shirye suna nuna bindigoginsu Kazalika su na saka kira'a ta Alkur'ani mai tsarki, da kuma jawabin shugaban 'yan jihadi na IS Abu Bakr Al-Baghdadi, da na kakakin kungiyar Abu Mohammed Al- Adnani a cewar mazauna ganin na Syrte.

Sai dai a cewar wani tsohon jagoran na birnin Syrte, har kawo yanzu dai ba'a ga wadannan 'yan jihadi suna yawo cikin garin ba, amma kuma sun fara ne da kame wannan gidan rediyo don su samu isar da sakonni ga al'ummar birnin. Birnin na Syrte dai, na mai zama mahaifar tsohon shugaban kasar ta Libiya marigayi Mouammar Kadhafi.