Hare-haren 'yan jihadi na kara yawaita a Mali
July 16, 2018Talla
A 'yan watannin baya-bayan nan dai daruruwan fararan hulla ne da suka hada da Fulani da Abzinawa 'yan jihadi suka hallaka. Ko a yammcin ranar Lahadi ma dai wasu 'yan bindiga da suka saba gudanar da muyagun ayyukansu kusa da iyakar kasar ta Mali da Jamhuriyar Nijar, sun kai hari a garin Injagalane da ke yammacin birnin Menaka, kaman yadda wata sanarwa ta hadin gwiwa ta mayakan kungiyoyi biyu na Abzinawa da ke marawa sojojin kasar Faransa baya ta bayyana.
Mutanen dai dauke da makammai sun zo ne bisa babura lokacin da suka shiga garin na Injagalane kuma suka yi harbin kan mai uwa da wabi cikin jama'a inda suka kashe mutane 14 tare da kona motoci da babura da dama acewar hukumomin jihar ta Menaka.