1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Myanmar: An saki 'yan jaridar Reuters

Yusuf Bala Nayaya
May 7, 2019

Wa Lone da Kyaw Soe Oo sun bayyana kewaye da 'yan jarida lokacin da suke fita daga gidan kason nan na Yangon da ya yi suna wajen azabatar da wadanda aka tsare.

https://p.dw.com/p/3I3VF
Myanmar, Yangon: Freilassung der Journalisten Kyaw Soe Oo und Wa Lone
Hoto: picture-alliance/AP/T. Zaw

'Yan jaridar nan guda biyu da aka tsare saboda ba da rahotanni kan 'yan Rohingya  da ke fuskantar gallazawa a kasar Myanmar, sun fito daga gidan kaso da ake tsare da su a wannan Talata bayan da suka samu afuwar shugaban kasa da ke zuwa bayan sukar kasashe da dama na duniya kan Myanmar dalilin tsare 'yan jaridar.

Wa Lone da Kyaw Soe Oo sun bayyana kewaye da 'yan jarida lokacin da suke fita daga gidan kason nan na Yangon da ya yi suna wajen azabatar da wadanda aka tsare a cikinsa, bayan tsawon lokaci da suka samu a tsare.
Wa Lone dai ya nuna farinciki bayan ganawa da iyalansu.

Kame wadannan 'yan jarida dai a watan Disambar shekarar 2017 ya sanya sun yi suna aduniya kuma ya kara fito da yadda 'yancin fadin albarkacin baki ke ganin tasku a Myanmar karkashin jagoranci na wacce ke da lambar yabo ta zaman lafiya kuma jagorar al'umma Aung San Suu Kyi. Wa Lone daya daga cikin 'yan jaridar me shekaru 33, ya bayyana cewa aikinsu na ba da rahotanni ba gudu ba ja da baya.