1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan jarida sun yi zanga-zanga a ƙasar Togo

Usman ShehuMarch 14, 2013

Jami'an tsaro a ƙasar Togo sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da sabbin dokokin matsawa kafafen yaɗa labarai da gwamnati ta yi

https://p.dw.com/p/17yDU
A riot policeman attempts to disperse opposition protesters during clashes in Togo's capital Lome, August 21, 2012. Police in Togo fired tear gas and rubber bullets to try to disperse thousands of opposition protesters in the capital Lome on Tuesday, as tensions over upcoming legislative elections boiled over. REUTERS/Noel Kokou Tadegnon (TOGO - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
'Yan sandan kwantar da tarzuma a birnin Lome na kasar TogoHoto: Reuters

A ƙasar Togo jami'an tsaron sun yi amfani da hayaƙi mai sa ƙwalla wajen tarwatsa yan jarida da ke zangazanga. Yan jaridan dai na neman a soke sabuwar doka da ta ke yin tarnaƙi kan aikin jarida. Waɗanda suka shirya zanga-zangar sukace jami'an tsaro sun raunata wasu yan jarida a kusa da fadar shugaban ƙasa. Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar yan jaridan ƙasar Togo, yace sun zo fadar shugaban ƙasa ne domin su jawo hankalinsa bisa sabuwar dokar da aka yi kan kafafen yaɗa labarai. Tunda fari magajin garin birnin Lome, ya buƙaci da kada masu zanga-zangar su je kusa da fadar shugaban ƙasa bisa dalilan tsaro, amma suka yi watsi da shi, inda suka bada hujjar zanga-zangar ta su ta lumane ce. A watan jiya ne majalisar dokokin ƙasar Togo ta baiwa hukumar kula da kafafen yaɗa labarai, yan cin rufe kafar yaɗa labarai ba tare da neman izinin kotu ba.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi