1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jarida na kukan matsi daga hukumomin China

February 1, 2022

'Yan jarida da ake aika da rahotanni ga kasashen duniya daga China, sun koka da dumbin matsaloli da suke fuskanta a lokacin gudanar da ayyukansu a kasar.

https://p.dw.com/p/46LPd
China | Xinjiang Pressekonferenz
Hoto: Xing Guangli/Xinhua/picture alliance

Korafin 'yan jaridar dai daga China, shi ne yadda matakan hukumomin ke dakile kokarinsu na samar da sahihan labarai cikin lokaci.

Wata kuri'ar jin ra'ayi da aka yi, ta nuna cewa kashi 99% cikin 100 na masu aiko da rahotannin daga China sun ce aiki a China ya gaza hawa mizanin aikin jarida na kasa-da-kasa.

Wasu ma daga cikin manyan matsalolin da suke fuskanta, su ne na hana su takardun zama wato visa da tsananin sa ido da barazana iri-iri.

Wani sama da kaso 30 ma daga cikin su, sun ce ana hana su 'yancinsu na daukar labarai a wasu muhimman bukukuwa da ke faruwa a kasar ta China.