1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jarida 10 na cikin wadanda suka mutu a Kabul

Zainab Mohammed Abubakar
May 1, 2018

Kasashen duniya sun yi Allah wadan kisan 'yan jarida 10 cikin wadanda harin Afganistan ya ritsa dasu, wanda MDD ta bayyana shi da "harin da aka shirya kaiwa kafofin yada labaru kai tsaye".

https://p.dw.com/p/2wx3p
Afghanistan Selbsmordanschlag Kabul
Hoto: Reuters/O. Sobhani

Tagwayen hare-hare a birnin Kabul, ya kashe mutane 25 ciki har da dan jarida mai daukar hoto na kamfanin dillancin labaru na Faransa na AFP Shah Marai, da wasu 'yan jarida guda takwas, kana wani wakilin BBC ya rasa ransa a wani harin na daban a gunduwar Khost da ke gabashin Afganistan din.

Daya daga cikin maharan na Kabul dai ya fake da kasancewa dan jarida, wanda ya bashi damar shiga tsakaninsu kafin ya yi kunar bakin waken. Wannan dai shi ne hari mafi muni da ya ritsa da ma'aikatan kafofin yada labaru tun bayan kifar da gwamnatin Taliban, a cewar kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa ta Reporters without Border.

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya nuna bacin ransa kan harin, wanda  kungiyar fafutuka ta IS ta dauki alhakin aiwatarwa.