´Yan Islama a Pakistan sun yi kira da a yi zanga-zanga | Labarai | DW | 31.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan Islama a Pakistan sun yi kira da a yi zanga-zanga

Bayan mummunan farmaki ta sama da aka kai kann wata makarantar Islamiya a Pakistan, masu kishin Islama na wannan kasa sun yi kira da a gudanar da jerin zanga-zanga a fadin kasar baki daya. A wani hari na yaki da ta´addanci da suka kai a jiya litini sojin sama na Pakistan sun halaka mutane kimanin 80. Rundunar sojin kasar ta nunar da cewa ana amfani da wannan makaranta ne a matsayin wani sansani na horas da ´yan ta´ada. To amma a nasu bangaren, mazauna yankin sun rawaito cewa dukkan wadanda aka kashen farar hula ne wadanda ba su san hawa ba su san sauka ba. A kuma halin da ake ciki Yerima Charles na Birtaniya wanda a halin yanzu yake wata ziyara a Pakistan, ya soke rangadin da ya shirya kaiwa birnin Peshawar saboda dalilai na tsaro.