′Yan IS ta sace mutane 400 a Afghanistan | Labarai | DW | 17.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan IS ta sace mutane 400 a Afghanistan

Mayakan Kungiyar IS sun sace fararen hula 400 a birnin Deir Ezzor biyo bayan munmunan harin da suka kai da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 135 a birnin.

Daraktan Hukumar kula da kare hakkin bil Adama ta kasar ta OSDH Rami Abdel Rahmane ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mayakan Kungiyar ta IS sun kwashe mutanen wadanda akasarinsu mata ne da kananan yara mabiya tafarkin Sunna daga unguwar Al-Bgheliyeh da ke a kewayen birnin na Deir Ezzor zuwa yankunan da ke a karkashin ikonsu daga ciki har da mayakan wasu kungiyoyi masu mara wa gwamnatin Bachar al-Assad baya.

Wasu rahotannin baya-bayan nan kuma na cewa mutane akalla 40 akasarinsu mata a kananan yara sun halaka a cikin wani hari da wasu jiragen yakin gwamnatin kasar Siriya suka kaddamar a birnin Raqa babbar cibiyar Kungiyar IS a wannan Lahadi.